
Al'adun Gargajiya
Shirin yana kawo al'adun gargajiya na zamani da na da daga sassan duniya, yana nuna bambancin al'adu da yawan jama'a. Akwai kuma shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da ake gabatarwa a ranakun Asabar da Lahadi.
Épisodes

Jamhuriyar Nijar ta gudanar da bikin ranar Hausa ta bana a ƙasar
Shirin Al’adumu na gado a wannan makon ya sake waiwayar baukukuwan ranar Hausa ne ta Duniya, ranar da babban taronta ke gudana a dukkanin ranakun 26 ga watan Agusta duk shekara, to amma kasancewar bikin ya samu karɓuwa a gwamman ƙasashe ya sa bayan babban taron ake gudanar da wasu ƙarin bukukuwan ranar hausar ta Duniya a ƙasashe daban daban, ciki har da Jamhuriyar Nijar, inda aka gudanar da bikin

Muhawara kan banbance tsakanin ƙabilun Hausawa da kuma Fulani a Najeriya
Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon ya mayar da hankali kan zamantakewa da auratayyar ƙabilun Hausawa da Fulani, ƙabilu 2 da suka juye zuwa Hausa Fulani bayan zaman tare na tsawon shekaru musamman a Najeriya. A baya-bayan nan muhawara ta fara zafi kan buƙatar banbance ƙabilun biyu zuwa Hausa daban da kuma Fulani zalla, lamarin da ya ci karo da fahimtar wasu daga cikin ma

Batutuwan da bikin 'Ranar Hausa ta Duniya' zai mayar da hankali kai a bana
Shirin Ala'adunmu na gado a wannan mako ya mayar da hankali ne kan 'Ranar Hausa ta Duniya' 'lokaci na musamman da ake amfani da shi wajen tunatar da muhimmancin harshen Hausa da kuma Al’adun Hausawa. Ku danna alamar sautin da ke sama domin sauraron cikakken shirin tare da Abdoullaye Issa...........

Halin da ake ciki game da al'adar 'Yan Kama da ke neman ɓacewa a ƙasar Hausa
Shirin "Al’adunmu na gado, ya mayar da hankali kan fadi-tashin da ake yi don adana tsohuwar al'adar mawaƙan 'Yan Kama a ƙasar Hausa. Waƙoƙin 'Yan Kama salon fasaha ne na musamman da mawaƙan ke amfani da shi domin nishaɗantarwa, inda suke sauya shahararrun waƙoƙi su koma na maganar abinci ko cika tumbi. A cikin shirin, masana sun bayyana yadda waɗannan mawaƙa ke da ƙwarewa wajen sarrafa harshen Hau

Wane tasiri Chamfi ke da shi wajen gyarawa ko kuma ruguza aure musamman a zamanin baya
Shirin Al'adunmu na gado na wannan mako zai mayar da hankali ne kan yadda Chamfe-Chamfe ke shafar lamuran auratayya musamman a zamanin baya. Ku danna alamar sauraro domin jin cikakken shrin tare da Abdullahi Isa

Muhimmancin zurfafa bincike a dukkan fannoni gabanin aure
Shirin 'Al'adunmu Na Gado zai yi duba ne kan muhimmancin zurfafa bincike gabanin aure. Al’adun al’ummar Hausawa da ma mafi yawan al’ummomin da ke zaune a yankin arewacin Nigeria, sun sahale wa iyaye, gudanar da bincike kan yaron da ya nuna kai yana son ‘yarsu da aure, kamar yadda shima bangaren angon, kan yi bincike kan yanayin lafiya, tarbiyya da nasabar yarinyar. Irin wannan bincike, ya taimaka

Makomar makarantun gwaji na harsunan gida a Jamhuriyar Nijar.
Shirin wannan makon zai duba makomar makarantun gwaji na harsuna gida da suka haɗa harshen Hausa. A waɗannan makarantu, za a riƙa koyarwa da harsunan gida. Za a koya wa yara sana'o'i irin na gargajiya, a kuma koya musu adabin harsshe da sauransu.

Yadda Hausawa ke cin kasuwar abincin gargajiya a Saudiyya
Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoullaye Issa a wannan mako ya yi duba kan yadda Hausawa ke ɗabbaƙa al'adunsu ta hanyar hada-hadar abincin gargajiya a ƙasa mai tsarki ko kuma Saudi Arabiya. Kamar yadda ya ke sanannen abu, Hausawa kan rungumi mabanbantan sabbin al'adu amma yana matuƙar wahala a garesu su yi watsi da abincin da suturarsu, wannan ya sanya samun kasuwannin abincin gargajiya da dama

Yadda kiɗan Gurmi ke neman ɓacewa a ƙasar Hausa
Shirinmu na yau ya leƙa sassan arewacin Najeriya da Jamhuriyar Nijar, tare da duba yadda wani fitaccen kiɗan gargajiya, wato kiɗan Gurmi, ke fuskantar barazanar bacewa a fadin ƙasar Hausa. Shin me ke janyo haka, kuma wane canji fasahar zamani ta kawo? Gurmi, kayan kiɗa ne da aka sani tun kaka da kakanni, wanda ƙera ta hanyar amfani da ƙoƙon ƙwarya da aka rufe shi da fatar dabba, musamman fatar guz

Yadda Hausawa mazauna Jamus suka gudanar da gagarumin taron sada zumunci
Shirin Al'adun mu na Gado na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda Hausawa mazauna Jamus suka gudanar da wani gagarumin taro. Ku danna alamar Saurare domin jin cikakken shirin tare da Abdullahi Isa.

Gombe: Fulani sun yi taro kan warware matsalolin da ke ɓata musu suna
Shirin Al'adunmu na Gado a wannan mako, yayi tattaki ne zuwa garin Gombe, inda Al'ummar Fulani suka gudanar da wani taro na farfaɗo da Al'adunsu na Gargajiya, da kuma tattaunawa a kan hanyoyin da za a bi wajen maido da Tarbiyya, gami da zamantakewa kyakkyawa a tsakanin Fulanin da kuma sauran Ƙabilu.

Yadda al'ummar wani gari suka riƙe Al'adar da suke kira da "Sai kowa ya zo"
Shirin Al'adunmu na Gado na wannan mako tare da Abdoulaye Issa ya yi duba kan wata Al'ada da ake kira "sai kowa ya zo" a tsakanin al'ummar wani gari da ke Yankin Arewacin Najeriya. Shiga alamar sauti don sauraron karin bayani.......

Tasirin karance-karance Littattafan Hausa wajen ɗabbaƙa al'adun Hausawa
Shirin Al'adunmu na Gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon, ya mayar da hankali ne kan tasirin karance-karancen Littattafan Hausa a zamantakewar Al'ummar yankin. Irin waɗannan Littafai kuwa sun ƙunshi Magana Jari da jiki Magayi baya da Uwar Gulma da Shehu Umar kana Ruwan Bagaja, waɗanda dukkaninsu suka taimaka wajen fito da Al'adar Hausawa a fili. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken sh

Rawar da mayaƙa suka taka zamanin da a Masarautun ƙasar Hausa
Shirin Al’adun mu na Gado a wannan makon ya leka Jamhuriyar Nijar ne, inda ya duba batun da ya shafi mazajen dauri, musaman mayaƙan gargajiya a wannan zamani, jaruman da ke ƙarƙashin inuwar sarakunan gargajiya. Duk inda akwai masarautun gargajiya an san su da tarin mayaƙa da ke yin tsarin daka a cikin kowane irin hali don kare su. Wannan tsarin ne da ya samo sali tun zamani da ake yaƙe-yaƙe tsaka

Yadda kiɗan shantu ke ƙoƙarin ɓacewa duk da shaharar da ya yi a shekarun baya
Shirin Al'adun mu na gado na wnnann mako ya waiwayi kiɗan Shantu ne da ya shahara tsakanin Mata a shekarun baya, wanda bayan tasirin da ya yi a waccan lokaci a fagen nishaɗantarwa, kiɗan na Shantu ke neman ɓacewa a yanzu. A shekarun baya dai wannan kiɗa na Shantu ya shahara ne tsakanin mata a yankunan arewacin Najeriya musamman a makarantu ko ɗalibai da kuma wasu sassan Jamhuriyar Nijar. Ku latsa

Yadda bikin addinin gargajiya na Vodun ke gudana a Jamhuriyar Benin (2)
Shirin Al'adunmu na Gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon, ya ɗora ne a kan yadda aka gudanar da bukukuwan addinin gargajiya na Vodun a Jamhuriyyar Benin, bikin addinin gargajiya da ke da muhimmanci a ƙasar.

Yadda bikin addinin gargajiya na Vodun ke gudana a Jamhuriyar Benin
Shirin Al'adunmu na Gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon, ya yi tattaki ne zuwa Jamhuriyar Benin, inda ya halarci bukukuwan addinin gargajiya na Vodun, bikin da ke da muhimmanci matuƙa a ƙasar. Tun a bara ne aka ƙara wa'adin ranakun gudanar da wannan biki wanda ke samun mahalarta daga sassa daban-daban na duniya, inda alƙaluma suka nuna cewar a shekarar bara baƙi fiye da dubu 100 ne suka hal

Hausawan Turai na fuskantar barazanar ɓacewar harshe da al'adunsu
Shirin "Al'adunmu na gado" a wannan makon tare da Nura Ado Suleiman ya leƙa ne Masarautar Hausawa da ke nahiyar Turai, inda a makon Masarautar ta karɓi baƙuncin Mai Martaba Sarkin Daura Dakta Umar Faruk Umar da ya yi tattaki daga Tarayyar Najeriya, domin halartar bikin karrama Sarkin Hausawan na Turai da kuma naɗin wasu sabbin muƙaman na sarauta da suka shafi sassan nahiyar. Daya daga cikin kaluba

Yadda aka gudanar da bikin nuna al'adu na masarautar Jiwa a Abuja
Shirin Al'adun gargajiya na wanan makon tare da Abdoulaye Issa ya yi duba game da yadda aka gudanar da bikin al'adu na masarautar Jiwa a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shirin.......

Yadda aka gudanar da bikin naɗin sarautar sarkin Komadugu a Maraɗi
Shirin na yau ya yada zango jihar Diffa dake Jamhuriyar Nijar,yankin da aka gudanar da bikin nadin sabon sarkin Komadugu, wanda ya samu halartar baƙi daga ciki da wajen ƙasar. Diffa dai kamar dai yadda masana tarihi suka tabbatar, ana na nufin Diwa a harshen Kanuri kenan. Kalmar ta samo asali ne daga kalmar "Di wa Nallé wa," wadda ke nuna tsabtar jiki da dai sauran abubuwan da suka shafi maza da m

Yadda sana'ar sassaƙar Turmi ke fuskantar koma baya sabida ci gaban zamani
Shirin "Al'adun mu na Gado" na wannan makon ya yi duba ne akan sana'ar nan ta sassaƙar Turmin, wadda ke a matsayin sana'ar al'adun gargajiya, ko da yake a yanzu samar da na'urori da ke amfanin da Turmin keyi ya mayar da sana'ar baya matuka gaya. A baya duk macen da za'a kai gidan miji, akan hadata da Turmin babba da ƙarami kana da kuma na ƙarfe wanda za ta rika daka kayan ƙanshi wasu ma hatta K

Yadda ƴan siyasa ke katsalandan a harkokin masarautu a Najeriya
Shirin al'adun mu na gado na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda ƴan siyasa ke katsalandan a masarautun gargajiya a Najeriya. Danna alamar sauarre domin jin cikakken shirin tare da Abdullahi Isa

Bikin Kalankuwar farfaɗo da al'adun Hausawa a jihar Kano ta Najeriya
Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya mayar da hankali ne kan Kalankuwar farfaɗo da al'adunmu Hausawa a jihar Kano ta arewacin Najeriya, a wani yanayi da al'umma ke fuskantar matsalar gushewar tarin al'adu a mataki daban-daban. Yayin wannan bikin Kalankuwa dai an duba fannoni daban-daban na al'adu kama daga Kiɗan gargajiya da Waƙa baya ɓangarorin wasanni da dama, bikin d

Yadda al'adar ''Ƴar zaman Ɗaki'' ta zama tarihi tsakanin hausawa
Shirin Al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya mayar da hankali kan yadda sananniyar al'adar nan ta zaman ɗaki ke ƙoƙarin shuɗewa tsakanin al'ummar Hausawa. Shekaru aru-aru, da zarar an yi auren budurwa a ƙasar Hausa akan haɗata da ƙaramar yarinya da za ta yi mata zaman ɗaki, wanda a wasu lokutan anje kenan domin galibi aure ke raba wannan ƙaramar yarinya da gidan, kodayake wasu
Recommandé

Les podcasts du Média

Audrey Dana

Mille et une histoires

Contes des Soirs Perdus

Chroniques étranges - Histoires d'Horreur & Mystères

La société de minuit

Choses à Savoir TECH

Apprends l’anglais 🇬🇧 pendant ton sommeil 😴 1000 phrases pour débutants | avec 1000-words.com

Légendes urbaines

Pascal Praud et vous

Journal des sports

8 milliards de voisins