Accueil Podcasts Muhallinka Rayuwarka
Muhallinka Rayuwarka

Muhallinka Rayuwarka

RFI Hausa 24 Épisodes août 15, 2026

Wannan shirin na RFI Hausa yana wayar da kan jama’a da kuma ilmantar da su game da harkokin noma, muhalli da canjin yanayi. Yana ba da bayanai kan gurbacewar yanayi da kuma dumamar duniya. Har ila yau, shirin yana taimaka wa masu sauraro su fahimci yadda za su kare muhallinsu. Ana kuma tattauna batutuwan da suka shafi rayuwar yau da kullum da ci gaban aikin gona.

Épisodes

Ƙarancin yashin gini na haddasa rikici tsakanin jama'a da illa ga muhalli
Ƙarancin yashin gini na haddasa rikici tsakanin jama'a da illa ga muhalli août 15, 2026 00:20:32 A wannan makon shirin ya mayar da hankali ne kan yadda aikin gine gine ke haddasa bukatar yashi wanda nemanshi ke zama matsala tsakanin jama'a, da kuma illa ga muhalli da wurin noma da hanyoyin ruwa da sauransu. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...
Yadda dazuka ke taimakawa wajan kare muhalli
Yadda dazuka ke taimakawa wajan kare muhalli août 8, 2026 00:20:13 Shirin Muhallinka rayuwarka na wannnan mako tare da Nasiru Sani ya duba irin gudun mawar da ganzun daji ke bayarwa wajan kare muhalli daga matsalar  sauyin yanayi Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin......
Yadda dazuka ke taimakawa wajan kare muhalli
Yadda dazuka ke taimakawa wajan kare muhalli août 8, 2026 00:20:13 Shirin Muhallinka rayuwarka na wannan mako tare da Nasiru Sani ya duba irin gudun mawar da dazuka ke bayar wa wajan kare muhalli daga matsalar sauyin yanayi. Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.......
Matakan da manoman Nijar ke ɗauka a lokutan da aka fuskanci ƙarancin ruwan sama
Matakan da manoman Nijar ke ɗauka a lokutan da aka fuskanci ƙarancin ruwan sama août 2, 2026 00:19:27 A Jamhuriyar Nijar,manoman dai sun fara da taka tsan-tsan ne saboda tsila-tsillar saukar ruwan shukar da suke fuskanta da kuma yanda ake samun dogon lokaci kafin saukar wani ruwan bayan saukar na farko, abun dake sanya shukar da suka yi ta mutu a ɗan wani lokaci.
Illolin karancin gonaki kusa da jama'a da yadda ya shafi burin bunkasa samar da abinci
Illolin karancin gonaki kusa da jama'a da yadda ya shafi burin bunkasa samar da abinci juil. 25, 2026 00:19:16 Sau da dama, masu burin shiga harkokin noma a Nigeria kan canza tunaninsu, sakamakon rashin samun gonakin da za su noma kusa da gari, lamarin da kan tilasta su jingine aniyarsu ta yin noma. Gwamnatin Nigeria dai, ta sha kira ga ‘yan kasar da su koma gona, la’akari da yadda Allah ya albarkaci kasar da wadatattun filayen noma da kuma yanayi mai kyau da za a iya noma kowane irin nau’in kayan abinci.
Matsalar ambaliyar ruwa da kan dagula lamuran al’uma a Najeriya
Matsalar ambaliyar ruwa da kan dagula lamuran al’uma a Najeriya juin 20, 2026 00:19:24 Kamar kowace shekara, a bana ma ana hasashen samun ambaliyar ruwa a wasu ƙasashen yammacin Afrika, inda akan samu rasa rayuka da dukiya mai tarin yawa. A Najeriya, an sha samun hasarar rayuka a sanadin matsalar ambaliyar ruwan, da kan rutsa da wasu yankunan ƙasar.
Masana na ci gaba da tsoratar da al'umma game da illolin da ke tattare da gurɓatacciyar iska
Masana na ci gaba da tsoratar da al'umma game da illolin da ke tattare da gurɓatacciyar iska juin 13, 2026 00:19:58 A wannan makon shirin ya mayar da hankali ne kan tasirin gurɓatacciyar iska ga lafiyar halittu da muhalli wato air pollution a turance. Iska na gurɓa ta ne ta hanyoyi da dama, kama daga hayaƙin na’urori wato injina a masana'antu, zuwa tarkacen bola ko kuma ƙone wasu abubuwa, wanda su ke kawo cikas ga yanayin muhalli tare kuma da kawo tazgaro ga lafiyar ɗan Adam.
Kananan manoma a Najeriya na nan kan tsarin noma na kaka da Kakanni
Kananan manoma a Najeriya na nan kan tsarin noma na kaka da Kakanni juin 6, 2026 00:19:32 A yau wannan shiri zai ba da hankali ne akan yadda har yanzu, kananan manoma a Nigeria na nan kan tsarin noma na Kaka da Kakanni, lamarin da ake gani yana hana ruwa gudu wajen tabbatar da cimma burin kasar na kasancewa mai dogaro da-kai a fannin samun wadatar abinci.
Yawaitar takin jabu ya zamewa Manoman Najeriya ƙalubale a bana
Yawaitar takin jabu ya zamewa Manoman Najeriya ƙalubale a bana mai 23, 2026 00:19:32 Shirin 'Muhallinka Rayuwarka na wannan makon, ya tattauna ne da masu ruwa da tsaki kan sha'anin Noma, a kan matsalar yawaitar taki da kuma magungunan ƙwari na jabu, matsalar da ta zamewa manoman Najeriya ƙalubale babba a shekarar bana.
Sauyin Yanayi ya jefa Manoma cikin ruɗani kan lokacin da ya dace su fara shuka
Sauyin Yanayi ya jefa Manoma cikin ruɗani kan lokacin da ya dace su fara shuka mai 16, 2026 00:18:43 Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan makon ya tattauna na a kan yadda samun saukar Ruwan Sama na farko a bana ya jefa manoma a jihohin Arewacin Najeriya cikin ruɗani dangane da lokacin da ya dace su fara shuka. Wannan na zuwa ne a yayin da hukumar hasashen Yanayi ta Najeriya wato NIMET, da uma wasu masana ke gargaɗi game da yiwuwar ɗaukewar ruwan saman da wuri, lamarin da zai yi janyo tafka hasar
Yadda saukar ruwan sama na farko ya jefa manoma cikin ruɗani
Yadda saukar ruwan sama na farko ya jefa manoma cikin ruɗani mai 9, 2026 00:18:43 A yau wannan shiri zai ba da hankali ne akan yadda Ruwan sama na farko da aka samu a baya-bayan nan ya jefa manoma a jihohin Arewacin Najeriya cikin ruɗani da fargaba, yayin da hukumar hasashen yanayi ta ƙasa, NiMet, da masana ke gargaɗi game da tsagaitawar ruwan saman da wuri wanda zai iya lalata duk wani amfani da aka yi a wannan lokaci.
Matsalar karancin tsaftataccen ruwa, na ci gaba da addabar iyalai a sassan Nigeria
Matsalar karancin tsaftataccen ruwa, na ci gaba da addabar iyalai a sassan Nigeria mai 2, 2026 00:20:00 Matsalar nan ta karancin tsaftataccen ruwa, na ci gaba da addabar miliyoyin iyalai a sassan Nigeria, kila ko saboda rashin samun damar jan ruwan famfo a gidajensu, ko kuma rashin samun ruwan daga hukumomin samar da ruwan famfo na jihohinsu, duk da makudan kudin da gwamnatocin jihohin ke warewa, da sunan samar da ruwa wa jama’arsu. Wannan matsala ba kawai ta tsaya kan iyalai da kan rasa ruwan amfan

Recommandé