
Kasuwanci
Wannan shiri na RFI Hausa ne da ke duba yadda kasuwanci da tattalin arzikin duniya ke tafiya. Yana kawo sabbin dabaru da hanyoyin ci gaban tattalin arziki a ƙasashe daban-daban. Ana kuma jin ta bakin ƴan kasuwa da masana'antu dangane da halin da suke ciki.
Épisodes

Matatar matatar Ɗangote ta ƙaddamar da sayar da hannayen jarinta a hukumance
Shirin kasuwa akai miki dole na wannan makon ya maida hankali ne kan ƙaddamar da shiga matatar Ɗangote kasuwannin hannayen jarin Najeriya, a wani biki da aka gudanar a babban shelkwatan kasuwannin hannayen jarin Najeriya da ke Marina a birnin Legas, inda shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko da kansa ya kaɗa ƙararrawar buɗe shigar matatar a hukumance. Matatar ta sanya hannun jari biliy

Tasirin da saida hannun jarin matatar man Dangote ke da shi ga al'umma
Shirin kasuwa akai miki dole na wannan lokacin, ya maida hankali ne kan yadda matatar Dangote ta shirya buɗe ƙofifinta ga al’umma domin su mallaki wani kaso a matatar mafi girma a Afirka, bayan da a karon farko ta sanar da shiga kasuwar hannayen jari. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba...........

Sharhi kan kalaman Alhaji Atiku na maido da tallafin mai a Najeriya
Shirin ‘kasuwa akai miki dole’ a wannan mako tattauna ne kan wasu batutuwa da suka taso masu nasaba da siyasa da tattalin arziƙi a Najeriya, Inda muhawara ta kaure kan batun tallafin man fetur, bayan da ɗan takarar shugabancin ƙasar na jam’iyyar adawa ta ADC Alhaji Atiku Abubakar ya yi alƙawarini maido da tallafin man idan aka zaɓe shi a 2027, to amma nan da nan gwamnatin Najeriyar ta mayar da ma

Ghana ta zama ƙasa ta 6 a cikin jerin ƙasashen da ke samar da zinari a duniya
Shirin kasuwa akai miki dole na wannan makon ya maida hankali ne kan yadda Ghana ta zama ta shida a cikin manyan ƙasashe da suka fi samar da zinare a duniya, bayan zarce Amurka a alƙaluman yawan zinare da ƙasar ta yammacin Afirka ta hako a shekarar 2025 da ta gaba. To, amma menene tasirin kasancewar ƙasar ta ɗaya daga cikin manyan masu samar da zinare a duniya ke nufi ga talakawan Ghana da kuma ta

Me cigaban kasuwar hannayen jarin Najeriya ke nufi ga talakan ƙasar kashi na 2
Shirin 'Kasuwa a kai Miki Dole' na wannan makon tare da Ahmed Abba ya dora kan shirin makon da ya gabata, wanda ya mayar da hankali kan ci gaba da kasuwar hannayen jarin Najeriya ta samu, wajen zama ta ɗaya a duniya, kamar yadda mujallar Bloomberg ta sanar a ƙarshen watan Yulin wannan shekara ta 2026. To amma me cikin gaban kasuwar hannayen jarin ke nufi ga takan ƙasar?

Cigaban kasuwar hannayen jari na nufin rayuwa ta fara inganta ga talakan Najeriya?
A ƙarshen watan Yulin wannan shekara ta 2026, mujalar Bloomberg da ke bibiyar harkokin tattalin arzikin ƙasashen duniya, ta bayyana kasuwar hannayen jarin Najeriya a matsayin ta ɗaya a duniya a fannin dala, wajen yi wa ta Koriya ta Kudu fintinƙau. Masana tattalin arziki sun alakanta wannan gagarumin ci gaba da kasuwar ta samu da sauye-sauye masu tsauri da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi

Ghana ta yiwa ƙasashen Afrika fintinkau a fannin ci gaban hada-hadar kuɗaɗe ta wayar hannu
Shirin na wannan mako ya duba yadda Ƙasar Ghana ta zama jagaba a fannin hada_hadar kuɗi ta wayar hannu a Afirka, inda a wannan shekara kaɗai kamfanonin sadarwar wayar tafi da gidanka suka yi hada-hadar sama da Cidi biliyan 40. Ku danna lamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Ahmad Abba.

Illar cushen kusan naira tiriliyan 1 a kasafin kuɗin Najeriya ga tattalin arziƙi
Shirin Kasuwa Akai Miki Dole tare da Ahmed Abba a wannan mako, ya mayar da hankali ne kan yadda aka gano cushen kusan Naira triliyan ɗaya cikin kasafin kuɗin Najeriya na wannan shekarar ta 2026, domin sayen motocin alfarma da kuma ayyukan tallafa wa jama'a. Wannan na ƙunshe ne cikin wani rahoton da wata cibiyar da ke sa’ido kan yadda gwamnati ke kashe kuɗaɗen kasafi a Najeriya wato Tracka. Cibiya

Matakin matatar Ɗangote ya fusata ƙungiyar dillalan man fetur a Najeriya
Shirin a wannan mako tare da Ahmed Abba ya yi dubi ne kan matakin da ƙungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu a Najeriya ta sanar na dakatar da sayen mai daga matatar Dangote, sakamakon matakin da matatar ta ɗauka na fara sayar musu da man da take tacewa da dala maimakon Naira. Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.......

Rashin rassan bankuna ya tilastawa al'ummar karkara rungumar POS a Najeriya
Shirin kasuwa akai miki dole dake bibiyar harkokin kasuwanci da tattalin arziki na wannan makon tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan yadda ci gabar fasahar zamani da aka samu a fannonin haɗar-haɗur ƙudi a Najeriya, ke shafar al’ummomi a yankunan ƙarƙara.

Ana samun ƙaruwar cin bashin kuɗin kiran waya tsakanin jama'ar Najeriya
Shirin "Kasuwa Akai Miki Dole" na wannan makon tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan yadda ƴan Najeriya suka rungumi ɗaukar bashin kiran waya, wanda wani rahoto ya ce, a bara kaɗai anci bashin kiran waya da ƙudinsu ya kai Naira Tiriliyan 4 da biliyan 61. Wasu bayanai da cibiyar fintech firms Optasia mai tattara alƙaluman shige da ficen kuɗaɗen layukan sadarwa ta fitar a baya-bayan nan, ya

Yadda tattalin arzikin Ghana ke haɓɓaka sannu a hankali
Yau shirin ya mayar da hankali ne dangane yadda tattalin arzikin ƙasar Ghana ke ci gaba da ɓunƙasa sannu a hankali. Ku danna alamar sauraro domin cikakken shirin tare da Ahmad Abba.

Koken ƴan Najeriya kan yadda bankuna ke zare musu kuɗi daga asusun ajiyarsu
Shirin Kasuwa Akai Miki Dole tare da Ahmed Abba a wannan mako ya yi dubi ne kan yadda ƴan Najeriya, ke nuna fushinsu dangane da zargin cire musu kuɗi ba bisa ka’ida ba daga asusun bankunansu. Miliyoyin 'yan Najeriya da yanzu haka ke fuskantar hauhawan farashin kayayyaki da kuɗin sufuri, da kuma rashin tabbas ga makomarsu a fannin tattalin arziki, caje-caje da dama da bankuna ke yi a asusun ajiyars

Yadda ƴan kasuwa a Najeriya suka jingine harakokinsu saboda tsadar sufuri
Shirin Kasuwa akai miki Dole na wannan mako tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan yadda a Najeriya, 'Yan kasuwa da dama suka fara jingine harkokinsu saboda yadda tsadar sufuri ke cinye ribar da suke samu, wasu lokuta har da jarinsu . Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.......

Yadda tsadar sufuri ya tilastawa 'yan kasuwa jingine sana'o'insu a Najeriya
A yau shirin ya mayar da hankali ne kan yadda a Najeriya, 'Yan kasuwa da dama suka fara jingine harkokinsu saboda yadda tsadar sufuri ke cinye ribar da suke samu, wasu lokuta har da jarinsu . Sannu a hankali, irin hada-hadar da aka saba gani tsakanin mafi yawan kasuwannin Nigeria na neman zama abun tarihi, sakamakon yadda ‘yan kasuwa masu tarin yawa suka jingine harkokinsu na kasuwanci saboda tsad

Damarmaki da kuma ƙalubalen da manoman Albasa a arewacin Kamaru ke fuskanta
Shirin kasuwa akai miki dole na wannan makon, ya duba ƙalubale da kuma damammaki a ɓangaren noman albasa a arewacin Kamaru. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Ahmad Abba.

Matakan da bankin CBN ke ɗauka na sake fasalin tsarin harkokin kuɗi a Najeriya
Shirin Kasuwa akai miki doke na wannan mako ya yi duba ne kan matakan da babban bankin Najeriya CBN ke ɗauka na sake fasalin tsarin harkokin kuɗaɗe, domin rage hauhawan farashin kayayyaki a kasuwanni da kuma daga darajar kuɗin ƙasar wato Naira, ta hanyar rage kuɗaɗe da ke yawo a hannun jama’a. Babban Bankin Nigeria, ya fito da bakin alƙalamin adadin kuɗaɗen da ke bankuna da waɗanda ake hada-hada d

Yadda matsalolin tsaro ke kassara kasuwanci a arewacin Najeriya
Shirin na wannan makon ya mayar da hankali ne kan irin fargabar da 'yan kasuwar arewacin Najeriya da ke fatauncin kayayyaki zuwa wasu sassan jihohi ke ciki, sakamakon ayyukan bata gari da ke tare hanya wanda a wasu lokuta kan kai ga rasa rayuka. Abune da aka saba gani, ‘yan kasuwar dake hada Hada tsakankin jihohi daga wannan kasuwa zuwa waccan ko tsakanin kasuwannin kauyuka. To sai dai Kuma irin w

Yadda matasa ke fatan cin gajiyar yarjejeniyar tattalin arziki tsakanin Nijar da Algeria
Matasa a Agadez da ke arewacin Jamhuriyar Nijar na cike da fatan cin moriyar sabuwar dangatakar da aka kyautata tsakanin kasar da makwabciyarsu Aljeriya. Ku danna alamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Ahmad Abba.

Koma bayan da kasuwancin duniya ya fuskanta sakamakon rikicin Gabas Ta Tsakiya
Shirin "Kasuwa Akai Miki Dole" tare da Ahmed Abba a wannan mako ya ɗora ne kan inda ya tsaya a makon jiya, game da gagarumin koma baya a fannin kasuwanci da tattalin arziki da duniya ke fuskanta masamman a bangaren makamashi, sakamakon yaƙin da kawancen Amurka da Isra’ila suka kaddamar kan Iran, da kuma martinin jamhuriyar musuluncin kan Isra’ila da muradun Amurka a kasashen labarawa suka janyo. A

Yadda yaƙin Iran ya haifar da koma baya ga tattalin arzikin Duniya
A yau shirin Kasuwa A kai Miki Dole na wanan mako tare da Ahmad Abba ya mayar da hankali ne a kan yadda Yaƙin da kawancen Amurka da Isra’ila suka kaddamar kan Iran, da hare-haren mayar da martini na jamhuriyar musuluncin kan yahudun Isra’ila da muradun Amurka a kasashen labarawa suka janyo gagarumar koma baya a fannin kasuwanci da tattalin arzikin duniya masamman a bangaren makamashi. Ku latsa

Yadda aka gudanar da taron tattalin arzikin a Akwa Ibom
Shirin Kasuwa A kai Miki Dole na wanan mako tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali kan taron taron tattalin arziki da ya gudana a farkon watan Fabarairun da ya gabata a jihar Akwa Ibom da ke kudancin Najeriya. Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.....

Najeriya da China sun yi bukin cika shekaru 55 da hulɗar diflomasiyya
Shirin 'Kasuwa a kai Miki Dole' na wannan mako tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan tasirin tattalin arziki dangane da alaƙar China da Najeriya da a makon jiya aka yi bikin cika shekaru 55 da faro hulɗar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu. Najeriya da China sun sake jaddada karfafa dangantakar diflomasiyya da ke tsakaninsu yayin da kasashen biyu ke bikin cika shekaru 55 da fara huldar di

Yadda buɗe iyakokin Najeriya da Nijar zai taimaka wajen haɓaka kasuwanci
Shirin Kasuwa Akai Miki Dole tare da Ahmed Abba a wannan mako ya yi dubi ne kan wani sabon yunkuri na kara inganta alakar kasuwanci tsakanin Najeriya da Nijar inda hukumar kwastom a jamhuriyar Nijar tayi tattaki zuwa Najeriya don tattaunawa hanyoyin da za’a bi don saukaka hada-hadar kayayyaki tsakanin kasashen biyu. Babban Kwanturolan Hukumar Kwastam na Najeriya Adewale Adeniyi, ya sake jaddada an











